Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
JKS da jam'iyyar kwadago ta jamhuriyar Congo sun gudanar da kwas na tattaunawa ta internet
2020-09-02 13:49:17        cri
A jiya ne JKS, da jam'iyyar kwadago mai mulka a jamhuriyar demokuradiyyar Congo, suka gudanar da wani kwas na tattaunawa ta internet.

Ministan kula da cudanyar kasashen waje, na kwamitin tsakiya na JKS Song Tao, ya yi bayani game da kashi na 3 na littafin "Kalaman Xi Jinping kan mulkin kasa, da tafiyar da harkokin kasa", kana ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya yi jawabi a gun taron kolin musamman kan hadin gwiwar Sin da Afirka, a fannin yaki da cutar COVID-19, wanda ya nuna hanyar raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a nan gaba.

Ya ce Sin ta dore muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin ta da jamhuriyar demokuradiyyar Congo, kuma JKS tana fatan gudanar da ayyukan da aka cimma daidaito a kan su, tsakaninta da jam'iyyar kwadago ta jamhuriyar demokuradiyyar Congo, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, da tabbatar da ra'ayin bangarori daban daban da adalcin duniya, da kuma sa kaimi ga neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da nahiyar Afirka.

A nasa bangare, babban sakataren jam'iyyar kwadago ta jamhuriyar demokuradiyyar Congo Pierre Moussa, ya godewa kasar Sin, bisa nuna goyon bayan ta ga kasarsa, wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a. Kana ya bayyana cewa, JKS ta jagoranci Sin wajen samun nasarori a fannin yaki da cutar COVID-19, matakan da kuma suka samar da fasahohi ga kasashen Afirka cikin har da kasarsa.

Ya ce jam'iyyarsa ta nuna goyon baya ga Sin, bisa kokarin ta na tabbatar da ikon mulkin kasa, da ikon samun bunkasuwa, tana kuma fatan kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da JKS, wajen tabbatar da odar kasa da kasa cikin adalci. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China