Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Congo Kinshasa yana son sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasarsa da Sin
2020-01-15 10:35:28        cri
Shugaban kasar Congo Kinshasa Felix Tshisekedi ya bayyana a jiya cewa, yana son yin kokari tare da kasar Sin wajen kara raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Tshisekedi ya nuna yabo ga dangantakar dake tsakanin Congo Kinshasa da Sin da hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, da al'adu da sauransu, a yayin da yake karbar takardar nadin sabon jakadan Sin a kasar Congo Kinshasa a wannan rana. Ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar kasarsa ce, ya ce an samu nasarori da dama a hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, wadanda suka amfanawa jama'arsu da kuma taimakawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Congo Kinshasa.

Shugaba Tshisekedi ya nuna godiya ga kasar Sin bisa ga gudummawa da goyon baya da take baiwa kasarsa, ya kuma yi maraba da kamfanonin kasar Sin da su zo kasar su kuma zuba jari. Ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da sada zumunta a tsakaninta da kasar Sin, kana tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

A nasa bangare, sabon jakadan Sin dake kasar Congo Kinshasa Zhu Jing ya bayyana cewa, Sin ta dade tana dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Congo Kinshasa bisa manyan tsare-tsare, kana tana son yin kokari tare da kasar wajen sada zumunta da fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni don sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa zuwa wani sabon mataki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China