Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Congo
2019-12-20 19:18:52        cri
A jiya Alhamis ne mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Yang Jiechi, ya gana da shugaban jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso. Yayin zantawar su, Yang ya ce Sin da Congo kawaye ne, abokan hulda ta gari, kuma 'yan uwan juna. Ya ce karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kudurorin da aka amincewa, yayin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, sassan biyu za su kara fadada hadin gwiwa a sassa daban daban.

A nasa bangare, Mr. Sassou ya ce kasarsa na martaba kawance dake tsakaninta da Sin. Har ila yau, al'ummar kasar na jinjinawa tallafin da Sin ke samarwa kasar a tsawon lokaci, musamman irin taimakon jin kai da Sin din ta samarwa Congo a baya bayan nan, sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan kasar.

Shugaba Sassou ya kara da cewa, Congo za ta ci gaba da shiga a dama da ita, cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", tana kuma burin karfafa hadin gwiwa mai inganci a muhimman sassa, ciki hadda fannin noma, da samar da ababen more rayuwa, da kayayyakin bunkasa masana'antu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China