Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan: zaman lafiya ya fi zama dan sarki
2020-09-01 17:13:52        cri

Hausawa na cewa, zaman lafiya, ya fi zama dan sarki. Wato dukkan wani jin dadi da karfin iko, ba komai ba ne idan babu zaman lafiya.

Yayin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin da kungiyoyi masu dauke da makamai a Sudan, ana fatan zai zama mataki mai inganci na kawo karshen rikicin da ya shafe tsawon shekaru 17 a kasar ta Sudan.

Kasar Sudan ta sha fama da matsaloli daban-daban, kama daga rashin tsaro zuwa tabarbarewar tattalin arziki da rashin ababen more rayuwa. Baya ga na baya-bayan nan, wato zanga-zangar da ta hambarar da mulkin tsohon shugaba Bashar al Assad a watan Afrilun bara.

Duk da cewa ana sa ran cimma wannan yarjejeniya tun a bara, zuwanta a yanzu ma, abu ne da ake matukar maraba da ita, duba da cewa, ana sa ran za ta kawo karshen takaddama tsakanin 'yan tawaye da kuma gwamnati, tare da zama tubulin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

A cewar MDD, tun bayan da 'yan tawaye suka dauki makamai a kasar a shekarar 2003, rayukan mutane 300,000 ne suka salwanta, baya ga asarar tarin dukiyoyi da tilastawa dubban jama'a tsarewa gidajensu.

Cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, wata gagarumar nasara ce ga gwamnatin riko na kasar da ta karbi mulki a shekarar 2019.

Duk da cewa wasu bangarori na 'yan tawayen sun ki amsa tayin, akwai kyakkyawar fatan cewa, idan har aka aiwatar da yarjejeniyar, kuma dukkan bangarorin suka girmama matsayarsu tare da sauke nauyin dake wuyansu, akwai yuwuwar su ma ragowar su shiga a dama da su, lamarin sa zai kai al'ummar kasar ga matsayin da suke muradi.

Ba a samu ci gaba cikin yini ko kwana guda, don haka, hakuri daga al'ummar kasar da ma sauran bangarori masu ruwa da tsaki na da matukar muhimmanci.

Hakika idan aka kiyaye wannan yarjejeniya ta zaman lafiya, za ta zama tamkar wani mafari na samun kyautatuwar al'amura a kasar, kama daga zaman lafiya, zuwa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da samun ababen more rayuwa har ma da ci gaba mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China