2020-05-25 17:39:55 cri |
Bayan sauraron kalaman da mista Wang ya gabatar, wasu masana da manyan jami'ai na kasashen Afirka, sun nuna amincewa da manufar da kasar Sin ta gabatar, tare da nanata cewa, yunkurin adawa da dunkulewar duniya, da neman daukar matakan kariya na kashin kai, ba shi da alfanu ko kadan. Cikin wadannan manyan kusoshin, har da wani shehun malami mai nazarin batutuwa masu alaka da Afirka da Sin daga tarayyar Najeriya, mista Adekunle, wanda ya ce ya gamsu da kiran da kasar Sin ta yi na kafa al'umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama ta fuskar kiwon lafiya, saboda wannan aikin ya shafi ingancin zaman rayuwar daukacin dan Adam. A cewarsa, yanzu haka dukkan mutanen duniya na kokarin yaki da annobar COVID-19, kana ba za a samu nasara a wannan yunkuri ba muddin ba'a yi watsi da bambancin kabila, da nuna kiyayya, kana a kuma karfafa hadin gwiwa tsakaninsu kasa da kasa ba, don neman ci gaban al'ummun duniya baki daya.
Shi kansa shugaba Xi Jinping na kasar Sin a lokacin da ya halarci cikakken zaman taron 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa mai kula da tattalin arzikin kasar Sin, ya jaddada cewa, a halin yanzu, wasu kasashen duniya sun nuna ra'ayin kariyar ciniki, amma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan kare tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa da kuma raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa ra'ayin dimokuradiyya.
A nan gaba kuma, za ta ci gaba da neman bunkasuwa bisa ka'idojin bude kofa ga waje, da hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna, domin inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta fuska mai bude kofa ga waje da fahimtar juna da cimma daidaito da kuma cimma moriyar juna, ta yadda za a gina tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga waje. Hakika za'a iya cewa ra'ayi ya zamanto iri guda a tsakanin shugabannin Sin da na Afrika wajen nuna adawa da ra'ayin kashin kai a maimakon hada kai da juna domin cin moriyar juna don a gudu tare a tsira tare kasancewar hannu daya baya daukar jinka.(Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China