Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban direktan kungiyar WTO ya yi murabus kafin cikar waadinsa
2020-09-01 14:20:59        cri

A jiya ne babban direktan kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO Roberto Azevedo, ya yi murabus gabanin cikar wa'adin aikin sa, shi ne kuma direktan kungiyar na farko da ya yi murabus kafin cikar wa'adinsa, tun kafuwar kungiyar a shekarar 1995.

A sakamakon hakan, aikin zaben sabon direktan kungiyar, a yanzu ya zama daya daga cikin ayyukan dake gaban komai ga WTO. A halin yanzu, 'yan takara daga Mexico, da Najeriya, da Masar, da Moldova, da Koriya ta Kudu, da Kenya, da Saudiyya, da kuma Birtaniya, suna neman zama sabon direktan kungiyar.

Majalisar zartaswar kungiyar, ta tabbatar da za a gudanar da zaben direktan na ta, tsakanin 'yan takara takwas cikin zagaye uku, a tsawon watanni biyu, tun daga ranar 7 ga wannan wata.

A cikinsu, 'yar takara daga Kenya Amina C. Mohamed, ta samu goyon baya mafi yawa, kuma 'yar takara daga Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta zama na biyu. Su biyun tare da dan takara daga kasar Masar Abdel-Hamid Mamdouh su ne daga nahiyar Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China