Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban daraktan WTO mai barin gado ya ce akwai jan aiki a gaban kungiyar
2020-07-24 10:35:13        cri

Jiya Alhamis, babban daraktan hukumar tattalin arziki da cinikayya ta duniya WTO mai barin gado ya ce hukumar tana fuskantar matukar matsin lamba, inda ya bukaci a kafa sabbin dokoki, da yin garambawul, da kuma aiwatar da hadin gwiwar bangarori daban daban a matsayin matakan da za su share hanyar cigaban kungiyar.

A jawabinsa na ban kwana ga babban taron majalisar gabanin saukarsa daga shugabancin hukumar a ranar 31 ga watan Augasta, babban daraktan na WTO Roberto Azevedo ya ce, kungiyar ta cimma nasarori masu yawa wadanda za'a yi alfahari da su. Sai dai ya ce, akwai abubuwa masu tarin yawa da ya kamata a aiwatar da su.

Ya ce, a yanzu mambobin kungiyar suna da wani tubali da za su iya gina sabbin dokoki da ingantaccen tsari, ba tare da sun mance da batun hadin gwiwar bangarori daban daban ba, da kuma muhimman batutuwan da ya zama tilas a warware su baki daya.

Wannan kwararren jami'in diflomasiyyar kasar Brazil ya sanar a watan Mayu cewa, zai kawo karshen wa'adinsa na biyu a shugabancin kungiyar watanni 12 gabannin cikar wa'adin bayan ya shafe shekaru 7 yana shugabantar hukumar. Akwai 'yan takara kimanin 7 da za su fafata domin neman maye gurbin Azevedo, kuma tuni suka gabatar da bukatarsu ga babbar majalisar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China