Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya bukaci a taimakawa Mali yayin da take kara fuskantar barazanar ta'addanci
2020-06-12 10:39:20        cri

Sakataren janar na MDD Antonio Guterres, ya jaddada bukatar kasa da kasa su ci gaba da taimakawa kasar Mali, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar manyan kalubalolin da suka hada da barazanar ayyukan ta'addanci da yaki da annobar COVID-19 a kokarin da kasar ke yi na neman warware rikicin siyasa kasar.

Babban jami'in MDD ya gabatar da jawabi a taron kwamitin sulhun MDDr da aka gudanar game da batun kasar ta yammacin Afrika, inda aka bayyana shirin wanzar da zaman lafiyar MDD a kasar da aka fi sani da MINUSMA, a matsayin yanki mafi hadari ga ayyukan MDDr inda take tallafawa gwamnati tun a shekarar 2013.

Guterres ya fadawa ministoci da jakadu da suka halarci taron cewa, aikin gina kasar Mali mai zaman lafiya da tsaro yana bukatar hadin gwiwar dukkan bangarori tare da dorawar tallafin shirin MINUSMA. Ya ce sun yiwa al'ummar kasar Mali da yankin Sahel alwashin samar musu da kyakkyawar makoma a nan gaba.

Kamar yadda yankin Sahel yake, kungiyoyin 'yan ta'adda da bata gari suna kara fadada ayyukansu ne a kasar Mali.

Yayin hare haren baya bayan nan da aka kaddamar a Mopti, shiyyar tsakiyar kasar mafi fama da rikici, an hallka rayukan mutane akalla 100.

Ko da yake, gwamnatin kasar Mali tana ci gaba da kokarin shawo kan rikice rikicen, Guterres ya bukaci hukumomin kasar su kara daukan kwararan matakai domin kawo karshen tashe tashen hankulan dake addabar kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China