Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me Ya Sa Kabilanci Ke Ci Gaba Da Addabar Amurkawa
2020-08-31 22:12:29        cri

A kwanakin nan, ana ta gudanar da zanga-zangar nuna kabilanci da bambancin launin fata a kasar Amurka. A ranar Asabar da ta gabata, dubun dubatar mutane sun bazama a kan tituna a garin Kenosha dake jihar Wisconsin, inda suka bayyana rashin gamsuwarsu da rashin adalci da aka nunawa Jacob Blake, bakar fata da wani dan sanda ya harbe shi da bindiga, lamarin da ya haddasa masa rauni mai tsanani. Sa'an nan a yayin gangamin da aka yi a birnin Washington a ranar Jumma'a da ta gabata, babban dan marigayi Matin Luther King, ya gaya ma dubun dubatar masu zanga-zanga cewa, kasar Amurka ba ta zama wata kasar da mahaifinsa yake burin gani ba, maimakon haka kasar ta shiga cikin wani yanayi na rudani.

Ko da yake an fara kawo karshen tsarin nuna wariyar launin fata a tsakiyar karnin 20, duk da haka, ba a samu daidaita huldar dake tsakanin kabilu daban daban daga asali a kasar Amurka ba. Sa'an nan barkewar cutar COVID-19 a wannan karo ya tsananta yanayin rashin daidaito tsakanin kabilu daban daban na kasar, da haddasa lalacewar huldar dake tsakanin kabilun, da karuwar aikace-aikacen karya doka sakamakon nuna kiyaya, lamarin da ya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al'ummar kasar. Wani babban dalilin da ya sa hakan shi ne yadda 'yan siyasan kasar Amurka suka kasa sauke nauyin dake bisa wuyansu, da yadda suke daukar wasu matakai na rashin hankali.

Wani yanayi na musamman game da nuna kabilanci na kasar Amurka, shi ne yadda 'yan asalin kasashen Turai farar fata, wadanda suka fi yawa a cikin al'ummar Amurka, ke rike da madafun ikon kasar, gami da daukar manufofi na nuna kyama ga sauran kabilun kasar. Wannan yanayi ya sa ake samun babban gibi tsakanin farar fata da sauran kabilun kasar, a fannoni daban daban. Ma iya cewa, ba a taba daidaita matsalar kabilanci a kasar Amurka ba, har ma wannan batu na kara tsananta aikace-aikacen nuna karfin tuwo da yake kara aukuwa a kasar.

Ko da yake an kawo karshen tsarin nuna bambanci ga bakaken fata 'yan asalin Afirka tun daga shekaru 1950 a Amurka, amma huldar da ke tsakanin al'ummomi daban daban ba ta kyautata ba. Barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta kara haifar da rashin daidaito a tsakanin al'ummomi daban daban a Amurka. Huldar da ke tsakanin al'ummomin kasar tana lalacewa, kana ana ta samun laifuffukan nuna tsana. Gibin da ke tsakanin al'ummomin kasar yana karuwa.

Wani muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne domin 'yan siyasan Amurka ba su yi kome ba dangane da lamarin, in ban da kara rura wutarwannan matsala. Fararen fata 'yan asalin Turai, wadanda ke da rinjaye a Amurka suke rike da ikon kasar baki daya, a don haka, a kullum suna raina sauran al'ummomin kasar, wannan shi ne halin musamman da Amurka take da shi ta fannin matsalar al'umma. Sabili da haka al'ummomi marasa rinjaye na Amurka suna fuskantar babban gibi a tsakaninsu da fararen fata 'yan asalin Turai a sassa daban daban na rayuwar al'ummar kasar, wanda ba za su iya kawar da shi ba. Ma iya cewa, Amurka ba ta taba kyautata matsalar nuna bambanci tsakanin al'ummomin kasar ba, kuma matsalar ta kara yin kamari sakamakon tashe-tashen hankali da ake ta samu a baya-bayan nan. (Bello, Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China