Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo bai cimma burinsa na rura wutar yakin cacar baki ba
2020-08-17 21:41:23        cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya kammala ziyarar aikin da ya kai kasashen Turai guda hudu da suka hada da kasar Czech, da Slovenia, da Austria da kuma Poland. Kamar yadda ya saba yi, a wannan karo, ya dukufa wajen yada "cutar siyasa" a wadannan kasashe, domin cin zarafin jam'iyya mai mulkin kasar Sin, da rura wutar farfado da yakin cacar baki.

Amma, bisa yadda kasar Amurka ta saba wajen kwashe moriyar kawayenta, yanzu, kasashen Turai ba su son zama masu goyon bayan manufar "Amurka da farko". Kuma, a wannan karon da Mike Pompeo ya kai ziyarar aiki a kasashensu, ko da yake, ya yi ta zargin kasar Sin bisa wasu dalilai marasa tushe, amma, kawayenta ba su yarda ba.

A lokacin da ya zargi kamfanonin fasahar 5G na kasar Sin, cewar wai za su kawo barazana ga tsaron kasashensu, firaministan kasar Czech Andrej Babis ya ce, kasarsa kasa ce mai mulkin kai, ba ta ganin tana fuskantar irin wannan kalubale. A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Austria Alexander Schallenberg ya bayyana cewa, kasarsa ta fi son kafa tsarin bayanai mai inganci, a maimakon tsara manufar hana wani kamfani musamman na wata kasa.

Haka kuma, a yayin da kasar Amurka ta ce, za ta tura sojojin da ta janye daga kasar Jamus zuwa tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai, kasar Czech ta ce, ba ta son sanin inda sojojin kasar Amurka za su tafi, muddin dai ba za su zo kasarta ba. A hakika dai, kasar Amurka ba ta samu fahimtar siyasa da kasashen dake tsakiya gami da gabashin yankin Turai ba, wadannan kasashe masu neman 'yanci a fannin diflomasiyya ba za su yi hadin gwiwa da Mike Pompeo ba.

Kasar Sin da kasashen dake tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai ba su taba yin sabanin siyasa ba cikin tarihi, kuma suna da moriyar iri daya a fannin hadin gwiwar albarkaru, da fasahohi, da kuma kasuwanni da sauransu.

A halin yanzu, da ake fama da matsalar koma bayan tattalin arziki da kariyar ciniki, babu wata kasa a yankin da za ta so katse huldar ciniki a tsakaninta da kasar Sin.

Yanzu haka kasashen dake tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai sun cimma ra'ayi daya cewa, kasar Sin ita ce abokiyar da ta kawo musu damammaki a maimakon kalubaloli. Wasu 'yan siyasa kamar Mike Pompeo da sauransu ba za su cimma burinsu na dawo da wani salo na yakin cacar baki ba, kuma, ci gaba da yin karya kan wannan batu, zai sa su zama masu aikata mugun laifi a tarihin duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China