Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu 'yan siyasan Amurka na cin amanar Amurkawa
2020-08-21 20:18:07        cri

A ranar 20 ga wata, an kama tsohon mai baiwa shugaban Amurka shawara Steve Bannon, da laifin aikata zamba a shirin tattara kudaden gina katangar dake iyakar kudancin kasar Amurka. A cewarsa, yana goyon bayan shirin shugabannin kasar Amurka game da gina katanga a kan iyakar kasa, amma, a zahiri yana satar kudaden kasar, domin gina kansa.

Wannan ya kara nuna cewa, ko da yake, wasu 'yan siyasan kasar Amurka su kan zargin kasar Sin, amma, hakan ya nuna cewa, su ne marasa mutunci. Su kan cimma muradunsu ta hanyar ci da gumin jama'a da gwamnatin kasarsu.

Kwanan baya, wasu jami'an kasar Sin sun jaddada cewa, ba kawai dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta shafi al'ummomin kasashen biyu ba, har ma, tana da tasiri kan zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban kasa da kasa. Sun ce, ya kamata Sin da Amurka su cimma ra'ayi daya wajen kiyayewa da kyautata dangantakar dake tsakaninsu, amma bai kamata a ci gaba da bata dangantakar dake tsakaninsu ba, domin wasu munanan muradun wasu 'yan siyasa na kasar Amurka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China