Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karairayin Mike Pompeo za su sa kamfanonin kasa da kasa barin Amurka cikin sauri
2020-08-20 10:21:42        cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ba da wata sanarwa a kwanakin baya, inda ya yi ikirarin cewa, ma'aikatar kasuwancin kasar za ta ci gaba da kayyade ikon kamfanin Huawei ta fuskar samun fasahohi daga Amurka, tare kuma da shigar da sassansa 38 daga kasashe 21 cikin wannan sabon takunkumi. Matakin da wadannan 'yan siyasar Amurka ciki hadda Mike Pompeo suka dauka zai illata dukkan sana'o'i a duniya, har da lahanta muradu da mutuncin kasar, daga bisani kuma zai haddasa kamfanoni daban-daban su bar Amurka cikin sauri.

A halin yanzu, gwamnatin Amurka ta yi iyakacin kokarin matsa lamba kan kamfanoni mallakar kasar Sin da burin hana wasu kamfanonin kimiyya da fasaha samun ci gaba a duniya, da kuma dauke hankalin jama'a daga gwamnatin saboda gazawarta ta daukar matakan da suka dace don yakar cutar COVID-19, har ma da kokarin kare mutuncin siyasar kasar da ta kusan tabarbarewa, ban da wannan kuma, akwai batun zaben da za a gudanar.

Barin kasuwanci da siyasa su yi halinsu, burin kamfanonin kasa da kasa ne. 'Yan siyasar Amurka kamar Mike Pompeo sun siyasantar da batun cinikayya da nufin aiwatar da manufar McCarthy cikin sha'anin kasuwanci, matakin da ya illata muradun kamfanonin kasa da kasa ciki hadda na Amurka. Kamata ya yi su daidaita tunaninsu su kuma fahimci cewa, ba za a iya samun matsayin kasa mafi girma a duniya bisa munanan hanyoyi ba, kana ba za a iya dakatar da bunkasuwar kimiya da fasahar kasar Sin ba ko kadan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China