![]() |
|
2020-08-18 13:00:03 cri |
A kwanakin baya, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ba da umarnin cewa, dole ne kamfanin ByteDance na kasar Sin ya katse huldarsa da kadarorin da suka baiwa Tik Tok damar gudanar da aiki a kasar Amurka, cikin kwanaki 90. Haka kuma ya ce wata manhajar wayar salula ta kasar Amurka da ByteDance ya saya a shekarar 2017 ta haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka.
Sai dai a nata bangare, jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya ta nuna shakku kan dacewar umarnin da shugaba Trump ya sanar, ko da yake wasu 'yan siyasar kasar Amurka na kallon Tik Tok a matsayin bangaren wani aiki na leken asiri.
A cewar jaridar, kasar Sin ba ta bukatar samun bayanai ta wayoyin salula na matasa. Sa'an nan yadda ake matsawa Tik Tok lamba, zai haifar da illa sosai. Saboda yadda aka dauki wannan mataki kan wani kamfani, bisa la'akari kadai da kasarsa, zai iya haifar da babbar barazana ga daukacin tsarin yanar gizo ta Intanet.
Har zuwa yanzu, babu wata shaidar da ta nuna cewa Tik Tok na samar da bayanai ga gwamnatin kasar Sin. Hakan na nufin, gwamnatin kasar Amurka ta dauki mataki kan wani kamfani na kasar waje ne bisa kin amincewarta da shi kawai. Hakan zai zama wani ra'ayi mai haifar da matsala ga kasar Amurka, ta la'akari da yadda kasar ke mallakar galibin manyan kamfanonin kimiyya da fasaha na duniyarmu.
"Idan kasar Amurka ba ta amince da wani kamfani na sauran kasashe ba, to, me ya sa za a ci gaba da amincewa da kamfanonin kasar Amurka?" in ji jaridar the Guardian. (Bello Wang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China