2020-08-19 13:45:56 cri |
Babban taron Jam'iyyar Democrat ta Amurka da ya gudana jiya da daddare, ya tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden, a matsayin dan takarar jam'iyyar a hukumance, a zaben shugaban kasar na bana, inda zai fafata da shugaban kasar mai ci, Donald Trump, dake neman wa'adi na biyu.
Bisa la'akari da barkewar COVID-19, an gudanar da manyan tarukan ne ta kafar intanet. Tawagogin wakilai 57 daga jihohi 50, da gundumar Columbia da yankunan ketare ne suka kidaya kuri'u daya bayan daya. Bayan sanar da sakamakon a North Carolina, Biden ya samu kuri'u 2,448, sama da 2,374 da yake bukata don zama dan takarar jam'iyyar a hukumance a zaben shugaban kasar Amurka na 2020. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China