Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Walmart na fatan Sin da Amurka za su warware bututuwan cinikayya dake tsakaninsu
2020-08-22 15:44:10        cri
Babban jami'in rukunin shagunan sayar da kayayyaki na Walmart, Dou Mcmillon, ya ce yana fatan kasashen Amurka da Sin, za su gina hadin gwiwa mai karfi a tsakaninsu, yayin da cutar numfashi ta COVID-19 ke barazanar wargaza yarjejeniyar cinikayya ta baya-bayan nan da kasashen biyu suka daddale.

Mcmillon wanda ya bayyana haka yayin zantawa a shirin kasuwanci na gidan talabijin na Fox mai suna "Mornings With Maria", ya ce yana fatan kasashen biyu za su hada kai. Ya ce "muna son yin kasuwanci a kasar Sin, kuma na san akwai Amurkawa da manoma da dama dake son yin kasuwanci da kasar ta Sin".

Jami'in ya ce, Walmart yana da kantuna da kulob-kulob sama da 400 a kasar Sin, kuma yana gina harkokin cinikayya ta yanar gizo a kasar ta Sin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China