![]() |
|
2020-08-25 10:43:46 cri |
Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana neman dauwamammen ci gaba mai inganci cikin sauri, da martaba ka'idar adalci da tsaro. Ya kamata a inganta musayar dake tsakanin bangarori daban daban na kasar Sin, da musayar dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, domin ya dace da halin da muke ciki. Sabon tsarin neman ci gaba yana nufin bude kofa da kuma yin musaya a tsakanin kasa da kasa.
Xi Jinping ya ce, ya kamata mu samar da sabbin damammakin ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire bisa kimiyya da fasaha, da tsayawa tsayin daka wajen yin kirkire-kirkire bisa ka'idar bude kofa ga waje. Haka kuma, ya dace a karfafa musayar kimiyya da fasaha tsakanin kasa da kasa.
Shugaba Xi, ya jaddada cewa, ya kamata mu kara karfinmu da daukar matakan kawar da tsohon tsarin dake hana bunkasuwarmu, da kyautata tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, domin inganta tsarin tafiyar da harkokin kasa, ta yadda zai dace da halin da muke ciki a sabon zamani. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China