![]() |
|
2020-08-20 15:49:54 cri |
Da yammacin jiya Laraba 19 ga watan nan na Agusta ne, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya jinjinawa daukacin ma'aikatan dake sahun gaba, wajen yaki da ambaliyar ruwa a daukacin sassan kasar Sin, bisa namijin kokarin su na dakile tasirin wannan annoba.
Shugaba Xi wanda ke ziyarar nazari, da bincikar halin da lardin Anhui ke ciki, ya isa sashen Luojiatuan na shingen tare ruwa ta Chaohu dake gundumar Feidong a birnin Hefei, don ganewa idanun sa yanayin ruwan tafkin Chaohu. Kaza lika ya ziyarci ma'aikatan dake aikin shawo kan ambaliyar ruwa, da dakarun rundunar sojin kasar ta PLA dake tallafawa wannan aiki mai muhimmanci a yankin. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China