![]() |
|
2020-08-20 15:42:17 cri |
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya karfafawa kamfanin Magang, wanda wani bangare ne na kamfanin sarrafa karafa na China Baowu, gwiwar amfani da damar dake akwai daga raya yankin mashigin tekun kogin Yangtze.
Yayin wani rangadi a lardin Anhui dake gabashin kasar Sin, shugaba Xi ya bukaci kamfanin na Magang, ya hada ayyukansa na gyare-gyare da neman ci gaba da aikin raya yankin mashigin tekun kogin Yangtze domin kokarin samun ci gaba yayin da yake gudanar da aikin. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China