Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 ya kai kusan miliyan 1.15
2020-08-21 09:48:40        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar a ranar Alhamis cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a Afrika ya kai 1,148,849, yayin da adadin mutanen da cutar ta kashe ya kai 26,664.

A cikin bayanan baya bayan nan da kwararriyar hukumar kiwon lafiyar ta kungiyar AU ta fitar ya nuna cewa, yawan mutanen da suka warke daga annobar COVID-19 ya kai 871,590 ya zuwa ranar Alhamis.

Afrika ta kudu ce annobar COVID-19 ta fi kamari a halin yanzu a nahiyar, inda adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 596,060. Sannan kasar ce ta fi yawan mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a Afrika, wanda ya kai 12,423.

A cewar Afrika CDC, kasar Masar ce take matsayi na biyu wadda take da mutane 96,914 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sannan mutane 5,197 da cutar ta kashe su. Najeriya ta samu adadin mutane 50,488 da suka kamu da cutar, kana mutane 985 sun mutu.

Shiyyar kudancin Afrika ce annobar ta fi yiwa illa, sai shiyyar arewacin Afrika da kuma yammacin Afrika, in ji hukumar ta Afrika. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China