Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An amince da muhimmancin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen yaki da annoba
2020-08-12 19:51:05        cri

A jiya Talata ne tawagar Sin dake kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da hadin gwiwar hukumar raya tattalin arzikin nahiyar ta MDD, suka gudanar da wata muhawara ta yanar gizo, game da muhimmancin hadin kan kasar Sin da kasashen Afirka a fannin yaki da annobar COVID-19.

Yayin muhawarar, dukkanin mahalarta sun amince cewa, goyon bayan juna, da kuma hadin gwiwa, su ne ginshikan yaki da annoba a mataki na kasa da kasa.

Da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban tawagar Sin a kungiyar AU Liu Yuxi, ya ce a lokacin da Sin ke cikin mawuyacin hali na yaki da cutar COVID-19, kasashe mambobin kungiyar AU, da sauran kasashen nahiyar, sun baiwa Sin din goyon baya mai ma'ana, ciki hadda samar da kudade da kayan aiki na jin kai, duk kuwa da wahalhalu da kasashen nahiyar ke fama da su.

A daya bangaren kuma, ita ma Sin ta tallafawa kasashen Afirka, da rukunoni da dama na kayan yaki da wannan annoba, ta kuma tura tawagogin jami'an lafiya zuwa kasashen Afirka 11, tare da gudanar da taruka ta bidiyo tsakanin kwararrun Sin da na Afirka, kana sassan sun yi musaya game da dabarun ganowa, da na jinyar masu dauke da cutar.

A nata bangaren, mataimakiyar babban magatakardar MDD, kana sakatariyar hukumar bunkasa tattalin arzikin Afirka ta MDD Vera Songwe, godewa kasar Sin ta yi, game da tallafin gaggawa kuma mai dorewa da ta baiwa Afirka, a gabar da nahiyar ke tsaka da yaki da COVID-19. Ta ce tallafin Sin game da ginin cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka ko Africa CDC, ya dada tabbatar da kyakkyawan kawance dake tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China