Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Darektan Africa CDC: Afirka tana samun ci gaba wajen samar riga kafin COVID-19
2020-08-14 12:45:01        cri

Darektan cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) John Nkengasong ya bayyana cewa, nahiyar tana samun gagarumin ci gaba a fannin samar da alluran riga kafin cutar numfashi ta COVID-19.

Da yake karin haske yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, John Nkengasong ya ce, Afirka ba ta nade hannu tana kallo ba. Yana mai cewa, yanzu haka tana tsara wasu dabaru na samar da alluran riga kafin cutar, tsarin da zai taimaka a kokarin da ake yi na samar da riga kafin da yadda za a ci gajiyar alluran a nahiyar.

Ya ce, yanzu ana kara samun wadanda ke harbuwa da cuta a ssasan nahiyar, inda ya jaddada cewa, taron manyan jami'ai na baya-bayan da aka shirya, wanda ya hallara shugabannin nahiyar da manyan jami'an hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka(AU) da na hukumar lafiya ta duniya(WHO), ya amince da wasu muhimman ginshikai guda uku, da shuka shafi samar da alluran riga kafi, da yadda kasashen nahiyar za su samu alluran.

A cewarsa, gishiki na farko shi ne, kafa wata kungiya mai karfi game da gwajin alluran a Afirka, ta hanyar amfani da dukkan albarkatu da Allah ya horewa nahiyar. Ginshiki a biyu, shi ne yadda za a samar da alluran. A halin yanzu, cibiyar tana sake fasalta hanyoyin gano wadanda za su bukaci alluran riga kafin a Afirka, da kasashen da ya kamata su fara amfana da riga kafin, da wadanda za a samarwa kudaden sayen riga kafin.

Matakai na uku da shiyyar za ta shigo game ga samar da riga kafin da cin gajiyarsa, shi ne yadda al'umma za su shiga a dama da su don cimma wannan buri.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China