Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta dakatar da Mali daga dukkanin harkokinta har sai an maido da aiki da kundin mulkin kasar
2020-08-20 09:53:44        cri

Hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta dakatar da kasar Mali daga shiga dukkanin wasu harkokin da suka shafi kungiyar, biyowa bayan tsare manyan jami'an gwamnatin kasar, ciki hadda shugaban kasa da firaminista da sojojin kasar suka yi.

Majalissar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta hukumar zartaswar kungiyar ce dai ta yanke shawarar dakatar da Mali a jiya Laraba, yayin taron ta na baya bayan nan game da halin da kasar ta yammacin Afirka ke ciki.

Cikin wani sako da majalissar ta wallafa a shafin ta na twita a jiya, ta ce Mali ba ta da damar sake komawa harkokin kungiyar, har sai ta koma aiki da kundin tsarin mulkin kasa. Kaza lika majalissar ta yi kira da a gaggauta sakin shugaba Ibrahim Boubacar Keita, da firaministan kasar, da ma sauran jami'an gwamnatin Malin da sojoji suka tsare ala tilas. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China