Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Keita na Mali ya yi murabus
2020-08-19 10:19:06        cri

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, wanda sojojin kasar sa ke tsare da shi a wani sansanin su, ya bayyana yin murabus daga mukamin sa. Keita ya bayyana hakan ne da almurun jiya Talata, tare da ayyana rushe majalissar dokokin kasar, da kuma gwamnatin da firaminista Boubou Cisse ke jagoranta.

A jiyan ne dai kungiyar ECOWAS, da AU, da kungiyar tarayyar Turai ta EU, da kuma MDD suka yi Allah wadai da tsare shugaba Keita, suna masu kira da a koma aiki da kundin tsarin kasar ba tare da wani bata lokaci ba.

A hannu guda kuma, wata sanarwa da kakakin babban magatakardar MDD Antonio Guterres wato Mr. Stephane Dujarric ya fitar, ta yi kira da aka koma aiki da doka da oda a Mali, tare da aiki da tanajin kundin tsarin mulkin kasar. Sanarwar ta rawaito Mr. Guterres, na sake nanata kiran warware matsalolin siyasar kasar ta hanyar shawarwari kuma cikin ruwan sanyi.

Daga nan sai Mr Guterres ya bayyana goyon bayan sa, ga yunkurin kungiyoyin ECOWAS da AU, na lalubo hanyoyin zaman lafiya, a yayin da ake fafutukar warware takaddamar siyasar kasar ta Mali, ciki hadda kokarin da wakilin musamman na MDD dake kasar ke yi a wannan fanni.

Guterres ya kuma ja hankalin masu ruwa da tsaki a kasar, musamman ma sassan jami'an tsaro da su kai zuciya nesa, tare da kare hakkokin bil Adama na daukacin al'ummar kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China