Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Matsayin Hong Kong na cibiyar hada-hadar kudi ba wata kyauta ce da aka baiwa yankin ba
2020-08-14 20:58:33        cri
A yau Juma'a, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya mayar da martani ga kalaman shugaba Donald Trump na kasar Amurka, wanda ya ce wai idan an ba gwamnatin kasar Sin cikakken ikon kula da yankin Hong Kong, yankin zai rasa matsayinsa na cibiyar kasuwanci da hada-hasar kudi.

Game da wadannan kalamai na Trump, Zhao ya ce matsayin da Hong Kong ya kai, na kasancewa wata cibiyar hada-hadar kudi ta duniya, ba kyauta ce da wata kasa ta baiwa yankin ba, wato dai ba wanda zai iya kawar da matsayin wannan yanki. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China