Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da sauran kasashe za ta samar da karin alfanu
2020-08-13 20:49:09        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin bude kofarta ga sauran kasashe, kana ya yi imanin cewa, hadin gwiwar da ake yi tsakaninsu, zai samar da tarin alfanu a nan gaba.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, kwamiti mai kula da cinikayyar da ake yi tsakanin Sin da Amurka na kasar Sin ya gabatar da sakamakon wani nazarin da ya yi a ranar Talata, wanda ya nuna cewa, kashi 70% na kamfanonin kasar Amurka da aka zanta da su, suna sa ran ganin ci gaban harkokin kasuwanci a kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa, kana wasu kashi 87% daga cikinsu, sun ce ba su da shirin janye jikinsu daga kasar Sin.

Dangane da wannan sakamako, mista Zhao ya ce, wannan batu ya nuna yadda mutanen sauran kasashe suke da cikakken imani ga ingancin kasuwanni, da muhallin kasuwanci na kasar Sin, da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba.

Zhao Lijian ya ce, duk da cewa annobar COVID-19 ta haifar da wasu matsaloli, amma tattalin arzikin Sin na da jajircewa sosai, kana yana da damar samun karin ci gaba. Jami'in ya nanata cewa, bisa yawan al'ummar kasar da ya kai biliyan 1.4, da kuma ingantaccen tsarin masana'antu, kasar Sin za ta yi kokarin kyautata dandalinta na bude kofa ga kasashen waje, da daidaita muhallin yin kasuwanci a kasar, ta yadda ci gaban tattalin arzikin kasar zai samar da karin damammaki ga kamfanonin kasashe daban daban. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China