Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin: Mike Pompeo ya saba da yin karya
2020-08-13 21:43:30        cri
Dangane da zancen da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya fada a kwanan baya, inda ya ci gaba da neman shafa bakin fenti kan kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mista Zhao Lijian, ya bayyana a yau Alhamis cewa, Mike Pompeo yana ta kokarin shafa kashin kaji kan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, gami da manufofin kasar na cikin gida da na harkokin waje, duk bisa son ransa ne, da kuma wani ra'ayin da ya rike na neman yin yakin cacar baki.

Dangane da zancen mista Pompeo, sau da dama kasar Sin ta riga ta bayyana matsayinta, saboda haka ci gaba da kokarin karyata maganarsa zai zama bata lokaci kawai.

Kafin hakan, Mike Pompeo ya fadi kalmomi marasa dadi kan manufofin kasar Sin a fannonin dakile cutar COVID-19, da batun Hong Kong, da na Xinjiang, da batun tekun kudu na kasar Sin, da dai sauransu, yayin da yake ziyara a kasar Czekh. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China