Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lauyan Najeriya: Yarjejeniyar rancen kudin Sin ta dace da ka'idar kasa da kasa
2020-08-13 10:44:26        cri

A ranar 11 ga wata, shahararren lauyen Najeriya kuma shugaban hukumar kwaskwarima kan dokoki ta jihar Legos Keml Pinhelro ya wallafa wani rahoto a jaridar "Today" mai taken "Da gaske ne Najeriya ta jinginar da 'yancin kasar?", inda ya bayyana cewa, rangwamen mulkin kai ka'idar dokokin kasa da kasa ce da aka amince, manufar tana nufin kotun wata kasa daban ba ta da ikon hukunta wata kasa mai cikakken 'yanci, an kuma aiwatar da manufar ce domin kare mutunci da daidaito da 'yancin kan kasa, wannan manufa ba doka ba ce. Tarihi ya nuna cewa, an riga an kayyade amfani da wannan manufa, misali a shekarar 1977, kotun Birtaniya ta taba kin amincewa da rokon rangwamen da babban bankin Najeriya ya gabatar, shari'ar ta nuna cewa, hukumar gwamnati ba ta da ikon rangwame yayin gudanar da cinikayya, an dauki matakin ne domin tabbatar da adalcin gudanar da harkokin kasuwanci.

Lauyen ya kara da cewa, a cikin yarjejeniyar rancen kudin da kasar Sin ta kulla da Najeriya, duk da cewa, an rubuta cewa, dole Najeriya ta daina amfani da ikon rangwame yayin gudanar da sulhuntawa, amma lamarin bai nuna cewa, Najeriya ta damka 'yancin kasar ga kasar Sin ba, kuma hakika ba haka ba ne, Najeriya ta daina yin amfani da ikon rangwamen sulhuntawa kawai, ba ikon mulkin kasa ba ne, bashin da kasar Sin take baiwa Najeriya mai rangwamen kudin ruwa, ya taimakawa Najeriya sosai, ma'ana Najeriya ta amfana matuka da bashin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China