Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta bayyana kudirin zurfafa alakar shawarar ziri daya da hanya daya da Sin bayan COVID-19
2020-06-22 19:25:36        cri

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Garba Shehu, ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna sanin ya kamata wajen taimakawa kasashen Afirka yaki da cutar COVID-19.

Malam Garba Shehu wanda ya bayyana haka yayin zantawa da kamfanin dillancin na Xinhua a Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya ce Najeriya na duba yiwuwar zurfafa alakar shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin bayan ganin bayan wannan annoba.

Shehu ya ce, tun lokacin da annobar ta barke a nahiyar Afirka, kasar Sin ta samarwa kasashen na Afirka kayayyakin lafiya tare da tura mata tawagogin ma'aikatan lafiya don yaki da annobar. Haka kuma masana kiwon lafiya na kasar Sin sun shirya taruka ta kafar bidiyo don raba fasahohinsu na yaki da cutar da takwarorinsu na kasashen Afirka.

Ya ce, da zarar an kawo karshen COVID-19, bangaren Najeriya zai zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a dukkan fannoni, tare da kara cin gajiyar hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya.

Haka kuma bangaren Najeriya yana maraba da kasar Sin don kara zuba jari a Najeriya da fadada hadin gwiwa da kasar Sin a fannin karfin samar da kayayyaki da sauran fannoni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China