Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Kasashen Afirka suna morewa daga bashin kasar Sin
2020-08-08 17:04:47        cri

Lawal Sale Maida, wani mai sharhi kan harkokin kasa da kasa na tarayyar Najeriya ya wallafa wani sharhi mai taken "Najeriya tana morewa daga bashin da kasar Sin ta samar" a jaridar Peoples Daily ta kasar, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da bashi ga kasashen Afirka ba tare da gindaya sharadin siyasa ba, a don haka kasashen Afirka da dama, ciki har da Najeriya suna samun babbar moriya daga bashin gatanci da kasar Sin take samarwa. Ya ce hakika tallafin da kasar Sin take samarwa da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka suna ciyar da tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen gaba, haka kuma suna kyautata rayuwar al'ummun kasashen matuka.

A cikin sharhin, ya kara da cewa, Najeriya ta samu basusuka sau 11 daga bankin shige da fici na kasar Sin tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020, inda ake amfani da wadannan kudade domin gudanar da manyan ayyukan kasar, duk da cewa, wasu mutane sun damu cewa, bai dace gwamnatin kasar mai yancin kai tana lamunin basusukan ba, amma idan an mayar da basusukan a kan lokacin da aka tsara, to babu bukatar damuwa kan lamari.

Sharhin ya kara da cewa, sakamakon nazarin da aka yi ya nuna cewa, a cikin shekaru goma masu zuwa, gwamnatin Najeriya tana bukatar akalla dalar Amurka biliyan 31 domin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, yanzu haka kasar Sin tana son samar da bashi ga Najeriya, kuma ko shakka babu bashin zai taimaka wajen kyautata yanayi na koma baya da Najeriya ke ciki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China