Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Najeriya ya wallafa wani rahoto mai taken "Sin da Afirka na hada kai domin dakile annoba"
2020-06-25 16:21:00        cri

Jaridun Leadership da Daily Mail da the Sun da wasu jaridun Najeriya sun wallafa wani rahoton da jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya rubuta tsakanin ranakun 23 zuwa 24 ga wata, inda jakadan ya yi nuni da cewa, a ranar 17 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron kolin shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka kan hadin gwiwa domin yaki da annobar cutar COVID-19, kuma ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken "Hada kai domin dakile annobar", tare musanyar ra'ayoyi da sauran shugabannin kasashen Afirka domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a bangaren dakike annobar, haka kuma sun cimma ra'ayi daya daga duk fannoni.

Bayan taron an fitar da hadaddiyar sanarwa, lamarin da ya nuna cewa, ra'ayin Sin da Afirka ya zo guda a kan muhimman harkokin da suke jawo hankulansu duka. Ban da haka, kasashen Afirka sun jinjinawa kasar Sin matuka saboda babban sakamakon da ta samu wajen hana yaduwar annobar a kasar, kana sun yabawa kasar Sin saboda tallafin da take samar musu gwargwadon karfinta yayin da kasashen Afirka ke kokarin dakile annobar, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta nuna godiya ga kasashen Afirka da ma kungiyar tarayyar Afirka saboda goyon bayan da suka nuna mata yayin da take dakile annobar, hakazalika kasar Sin ta yabawa kasashen Afirka saboda yadda suka tsara tsarin dakile annobar a fadin nahiyar, tare kuma da nada manzon musamman domin neman samun goyon bayan kasa da kasa, ta yadda za su rage illar da annobar ta haifar wajen ci gaban tattalin arziki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China