Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayin Xi Jinping game da batun matasa
2020-08-12 20:40:33        cri

 

Ranar 12 ga watan Agusta ita ce ranar matasa ta duniya. A wannan rana ta musamman, bari mu karanta wasu maganganun da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada dangane da batun matasa. Shugaban ya taba fadin cewa:

"Matasa za su tabbatar da makomar huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, saboda haka kasar Sin na kokarin taimakawa matasan bangarorin 2, don samar musu da karin guraben aikin yi, da damammaki na raya kansu. Ina fatan dalibai 'yan Afirka dake karatu a kasar Sin, za su yi kokarin koyon ilimi, daga bisani za su daukaka hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi. "

"Ina fatan ganin matasa na kasashe daban daban za su iya son duniyarmu, da kokarin raba fasahohi tsakaninsu, don sanya al'adu daban daban zama tare cikin jituwa, ta yadda za su samar da gudunmowa ga yunkurin kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga bil Adama."(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China