Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya ba da umarni a daina barnata abinci
2020-08-11 13:35:44        cri
Babban sakataren kwamitin koli na JKS, shugaban kwamitin sojan kasar kana shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya ba da wani muhimmin umarni na a daina barnata abinci. Yana mai nuni da cewa, ya ji bakin ciki da kaduwa da yadda ake lalata abinci, Ya ce, kowa ya san cewa, duk wata kwayar abinci, da wahalar aiki ne ake samunta. Ya ce, duk da amfanin gona mai yawa da aka samu a kasar Sin, ya kamata kullum mu yi taka tsan-tsan wajen adana abinci. Shugaba Xi ya ce, a wannan shekara, tasirin cutar numfashi ta COVID-19 da ta addabi duniya, ta fargadda da mu.

Shugaba Xi ya jaddada bukatar karfafa doka, da sanya ido, da daukar managartan matakai da bullo da matakai na dogon lokaci game da hana barnata abinci. Haka kuma ya kamata a kara Ilmantar da jama'a, da bullo da al'adar adana abinci da samar da wani yanayi na kunyata barnata abinci a cikin al'umma baki daya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China