Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NEMA ta ba da wani sabon gargadi na mummunan ambaliyar ruwa a Lagos
2020-08-12 13:20:48        cri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta bayar da wani sabon gargadi cewa, birnin Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, zai fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a wannan shekara, kuma matsalar na iya shafar a kalla mutane miliyan 8.

Da yake Karin haske kan wannan batu, jami'in hukumar mai kula da ofishin yankin Lagos Ibrahim Farinloye, ya bayyana cewa, akwai hasashen dake nuna cewa, wasu sassan jihar ta Lagos za su fuskanci ambaliyar ruwa. Yana mai cewa, yanzu haka, an nunawa miliyoyin mutane matakan tunkarar wannan bala'i da ma yadda za su jure tasirinta.

Jihar Lagos dai,tana daya daga cikin jihohin kasar dake fuskantar hadarin ambaliya, matsalar da ake fama da ita kusan a jihohi da dama na kasar.

Farinloye ya bayyana cewa, matsalar ambaliyar a Lagos, tana iya karuwa, saboda yadda ake sakar ruwa ba bisa ka'ida ba a wasu sassan jihar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China