Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta halaka masu yawon shakatawa a kasar Kenya
2019-09-02 14:09:22        cri
Kwamandan rundunar 'yan sandan yankin Rift Valley na kasar kenya, Marcus Ochola, ya tabbatar da mutuwar masu yawon bude ido 'yan kasar Indiya 5 da mai masu jagora dan kasar Kenya, lokacin da ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da motar da suke ciki a wurin shakatawa na Hell's Gate a garin Naivasha dake kasar ta Kenya.

Ochola ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, masu aikin jagoran, sun san cewa, ambaliyar ruwan tana kwararowa daga tsaunukan wajen, amma ba su karanta bayanan hasashen yanayi a yankin ba. Yanzu dai ana ci gaba da neman wadanda ke da sauran nunfashi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, daya daga cikin wadanda suka tsira daga bala'in, ya fargad da jami'an dake kula da gandun, bayan ya kubuta daga bala'in ambaliyar ruwa dake kwararowa cikin kwazazzbo.

Ochola ya bayyana cewa, ana ci gaba da aikin nema da ceto, amma yadda ruwan ke kara toroko yana haifar da tsaiko. Ya ce, an tura karin jami'ai zuwa gandun dajin, don hada gwiwa da tawagar masu aikin ceton.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China