Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar AU ta kaddamar da wani shirin taimakawa harkokin kasuwanci na Afirka
2020-08-12 09:47:01        cri

Hukumar raya kasashe ta kungiyar tarayyar Afirka (AUDA_NEPAP) ta kaddamar da wani shiri jiya Talata da nufin taimakawa kanana da matsakaitan kamfanoni na nahiyar Afirka (MSMEs), ta yadda za su iya gudanar da ayyukansu a gabar da ake fama da cutar COVID-19.

Da yake Karin haske game da shirin, babban jami'in hukumar ta AUDA-NEPAD, Ibrahim Assane Mayaki, ya bayyana cewa, shirin wanda hukumar AUDA-NEPAD ta kaddamar tare da hadin gwiwar rukunin bankin Eco, zai baiwa 'yan kasuwa a kasashen Afirka daban-daban, damar samun horo da damammaki na samun taimakon kudade, da na'urori na zamani da ake bukata wajen tafiyar da harkokin kasuwanci da kuma yadda za su gudanar da harkokinsu na kasuwanci a lokacin da duniya ke fama da annobar COVID-19.

Bugu da kari, shirin zai samar da wata dama ta sanya ido a harkoki na kasuwa da kwarewa, a yayin da ake taimakawa 'yan kasuwar amfana da damammaki ta samun kudaden da za su rika tafiyar da harkokinsu na kasuwanci.

Jami'in ya bayyana cewa, yayin da nahiyar ke fuskantar rashin tabbas a fannonin tattalin arziki da zamantakewar jama'a, sakamakon barkewar annobar COVID-19, shirin zai taimakawa kanana da matsakaitan kamfanoni a nahiyar, ta yadda za su jure har ma su tsaya da kafafunsu a wannan lokaci mai cike da sarkakiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China