Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin zata kara fadada dangantakar cinikayya da Najeriya: Jakadan kasar Sin
2019-05-26 16:35:04        cri
Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin fadada dangantakar kasuwanci da Najeriya, duk da rahotannin dake nuna ana cigaba da samun takaddamar kasuwanci tsakanin Sin da Amurka.

Labarin da jaridar Leadership ta samar ya ce, jakadan kasar Sin a Najeriya, Dr Zhou Pingjian, shi ne yayi wannan alkawari a yayin gabatar da wata lacca wanda ofishin jakadancin Sin ya shirya a Abuja a ranar Juma'a.

Yace duk da kasancewar kasashen Sin da Amurka manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, takaddamar ciniki dake tsakanin kasashen biyu ba zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya ba. A cewarsa, duk da irin damuwar da duniya ke nunawa game da tattaunawa cikini tsakanin Sin da Amurka, za'a cigaba da daukar matakai domin kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya.

"Tabbas zamu cigaba da kara fadadawa da bude kofa saboda mun yi imananin cewa bude kofa yana kara kawo cigaba, kana zama saniyar ware yana haifar da koma baya.

Ya kara da cewa, "Mun fahimci damuwar, Sin da Najeriya suna da kyakkyawar dangantaka kuma zamu dauki karin matakai domin bunkasa dangantakar".

Jakadan na Sin ya bayyana rashin jin dadinsa game da barkewar takaddamar cinikin wanda Amurka ta tayar da shi, ya kara da cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare kanta da kuma kare hakikanin moriyar kasuwancinta.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China