Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa da shiga harabar karamin ofishin jakadancinta dake Houston da Amurka ta yi ba tare da neman izini ba
2020-07-26 16:07:38        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a jiya Asabar cewa, kasarsa ta nuna matukar rashin jin dadi da kuma nuna adawa kan matakin kasar Amurka na shiga harabar karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston ba tare da neman amincewarta ba, kuma ta riga ta nuna matukar takaici game da hakan. Kana kasar Sin zata mayar da martani mafi dacewa kan batun.

A yammacin ranar 24 ga watan Yuli, masu amfani da dokoki na kasar Amurka sun yanke kudirin afkawa karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston. Game da haka, Wang Wenbin ya ce, ginin nan gini ne na ofishin jakadanci, kuma dukiya ce ta kasar Sin. Bisa yarjejeniyar huldar jakadanci ta Vienna da yarjejeniyar jakadanci ta Sin da Amurka, bai kamata kasar Amurka ta keta hurumin ginin karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston ba ta kowace irin fuska.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China