Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ce ta haddasa matsala tsakaninta da kasar Sin
2020-07-24 20:15:57        cri

Yau Jumma'a, yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yake tattaunawa da takwaransa na kasar Jamus ta kafar bidiyo, ya yi karin bayani kan huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka a halin yanzu.

A cewar ministan, Amurka ce ta haddasa matsala a tsakaninta da kasar Sin a halin yanzu. Kuma ta yi haka ne, a yunkurin dakatar da ci gaban kasar Sin baki daya. Kwanan baya kuma, wasu Amurkawa masu adawa da kasar Sin sun cusa tunanin kiyayya tsakanin Sin da wasu kasashe, ta hanyar tilasta wa wasu kasashe su goyi bayansu wajen nuna adawa da kasar Sin domin kiyaye muradun Amurka. Amma dukkan kasashe masu basira wadanda suke girmama 'yancin kai ba za su goyi bayansu ba.

Wang Yi ya kara da cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin ba ta son ta da fitina da Amurka, ba ta son nuna adawa da Amurka. Tana fatan kasashen 2 za su mutunta juna da hada kai domin kiyaye moriyar juna. Amma ya zama tilas kasar Sin ta kiyaye 'yanci, da mutuncin al'umma, ta kuma kare halaltattun hakkokinta na raya kasa, ta kuma kiyaye manyan ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa. Kasar Sin ba za ta biye sahun Amurka ba, kuma ba za ta yarda Amurka ta yi abin da ta ga dama ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China