Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
EU ta jaddada aniyar tallafawa WHO ta bukaci Amurka ta sauya tunanin yanke hulda da hukumar
2020-05-31 17:14:39        cri

Babban jami'in kungiyar tarayyar turai EU da babban jami'in diflomasiyyya sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, kungiyar za ta ci gaba da tallafawa hukumar lafiyar ta duniya (WHO), sannan sun bukaci gwamnatin Amurka ta sake tunani kan kudirinta na yanke alaka da hukumar ta WHO.

A ranar Juma'a shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar cewa, kasarsa ta yanke duk wata hulda dake tsakaninta da hukumar WHO, kana ta ayyana sauya akalar kudaden da take tallafawa hukumar zuwa wani bangaren na daban.

Ursula von der Leyen, shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Turai, da Josep Borrell, babban wakilin EU kan al'amurran kasa da kasa da manufofin tsaro, sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, ya kamata hukumar WHO ta ci gaba da ba da jagoranci wajen aikin dakile annoba a matakin kasa da kasa, a halin yanzu da kuma a nan gaba. Game da wannan, ana matukar bukatar goyon baya da kuma tallafi daga kowane bangare. A yayin da duniya ke fama da kalubaloli, yanzu lokaci ne da ya dace a hada gwiwa domin neman mafita tare. Dole ne a kaucewa duk wasu abubuwa da za su kawowa kasa da kasa mummunan sakamako.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China