Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Amurka za ta hanzarta ganin bayan COVID-19 tare da daina dora laifi ga Sin
2020-08-07 20:26:30        cri

Yau a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan Amurka za ta hanzatta ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19, a sa'i daya kuma, tana fatan wasu 'yan siyasar kasar za su daina dora laifi ga kasar Sin.

Rahotanni sun nuna cewa, a jiya Alhamis jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Terry Edward Branstad ya kai ziyara birnin Shanghai, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar annobar, kayayyakin da kasar Sin ta samarwa kasarsa sun ceto rayukan al'ummun kasar da dama, kana ya yi nuni da cewa, yana fatan kasashen biyu za su kara karfafa cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninsu, domin dakile illar da annobar ta haifar tare.

Kan wannan, jami'in kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana yayin taron ganawa manema labarai cewa, cututtuka masu yaduwa ba su san iyakar kasa ba, kana abokan gabn daukacin bil Adama ne, muddin a hada kai, sai za a cimma burin dakile cututtukan a kan lokaci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China