Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa da yadda Amurka ke dakushe manyan kamfanonin kere-kerenta
2020-08-06 19:12:23        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya sanar Alhamis din nan cewa, kasarsa tana adawa da yadda Amurka ke dakushe da neman hana manyan kamfanonin kimiya na kasar Sin gudanar da ayyukansu a kasar ta Amurka, ta hanyar amfani da ikonta ba bisa ka'ida ba. Yana mai kiran irin wannan mataki da 'halayyar Amurka ta muzgunawa" da nufin nuna matsayinta na neman mamaye manyan fasahohin kimiya.

Wang ya bayyana wadannan kalaman ne, yayin taron manema lanarai, lokacin da yake karin haske game da sanarwar baya-bayan da Amurka ta bayar, na haramta manhajar kasar Sin daga ci gaba da kasancewa a Amurka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China