Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin na adawa da sabon yakin cacar bakin da aka bullo da shi
2020-08-05 21:04:51        cri

A yau mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya zanta da manema labarai, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana adawa da sabon yakin cacar bakin da aka bullo da shi, saboda hakan ya sabawa babbar moriyar al'ummun kasashen biyu wato Sin da Amurka, haka kuma ya sabawa yunkurin ci gaban duniya.

Wang Yi ya kara da cewa, yanzu wasu 'yan siyasar Amurka suna shafawa kasar Sin bakin fenti ta hanyar baza jita-jita, domin lalata cudanya da zumunta da fahimta dake tsakanin sassan biyu, a don haka kasar Sin ba za ta amince da wannan makarkashiya ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China