Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin na adawa da yunkurin kawo baraka
2020-08-05 21:03:17        cri

A yau mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi zantawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa, yanzu haka an riga an shiga karni na 21, amma wasu suna kokarin kawo baraka, wannan lamari tamkar nuna raini ne ga hikima da ci gaban bil Adama, kana koma baya ne ga tarihi, a don haka galibin kasashen duniya, ba za su amince da wannan makarkashiya ba. Wang Yi ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin tana adawa da yunkurin kawo baraka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wata muhimmiyar shawarar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama domin daidaita sabanin dake tsakanin tsarin mulki da kabilu da wayewar kai iri daban daban, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari domin cimma wannan buri mai kyau ga daukacin bil Adama.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China