Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya yi kira da a kawar da barazanar nukiliya a nan gaba
2020-08-06 20:57:32        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterre ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi kokarin ganin sun samar da yanayin da nan gaba duniya za ta fita daga barazanar makamin nukiliya.

Guterres wanda ya bayyana haka cikin sakon da ya aiko ta kafar bidiyo ga bikin tunawa da zaman lafiya na Hiroshima, ya ce shekaru 75 da suka gabata, makamin nukiliya guda daya tak ya haddasa barna da mutuwar mutane da dama a wannan birni.

Ya ce, yana tuna kafa MDD a shekarar 1945, shekarar da makamin nukiliya ya fada a kan biranen Hiroshima da Nagasaki, tun farkon kafuwa da kudurorinta, majalisar ta fahimci bukatar kawar da makaman nukiliya daga doron kasa.

Sai dai, ya ce har yanzu ba a kai ga cimma wannan buri ba, yana mai cewa, kokarin mallakar makamai, da yin komai a bayyane da matakan da a bullo da su a lokacin yakin cacar baka da bayan haka, har yanzu suna haifar da barazana. A don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su kara karfafa matakan hana yaduwa da kwance damara. Jami'in na MDD ya kuma ba da misali da taron bitar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukuliya dake tafe a shekara mai zuwa a matsayin wata dama ga kasashe, da su dawo kan wannan manufa ta bai daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China