Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin za ta mayar da martanin da ya dace kan matakan Amurka marasa dacewa
2020-08-05 21:01:26        cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya bayyana cewa, manufofin kasar Amurka kan kasar Sin ya ci tura, tamkar tunanin yakin cacar baka.

Ministan wanda ya bayyana haka yayin zantawa da kamfanin dillancin larabai na Xinhua Larabar nan kan alakar Sin da Amurka, ya yi nuni da cewa, kalaman gazawar Amurka na kasa ganin dukkan kyawawan sakamakon da aka cimma a alakar Sin da Amurka cikin shekaru goma da suka gabata, ya nuna yadda ta jahilci tarihi da rashin martaba al'ummomin Sin da Amurkar.

Ya ce, wannan kwayar cutar siyasa ce, wadda jama'a a Amurka da duniya ke dasa ayar tambaya a kanta. Ministan ya kara da cewa, a cikin sama da shekaru 40 da wani abu da suka gabata, tun lokacin da kasashen biyu suka kulla da huldar diflomasiya a tsakaninsu, zuriyoyin sassan biyu sun yi aiki tare don ciyar alakar kasashen biyu gaba.

Wang ya jaddada cewa, a cikin shekaru 40, yayin da Sin da Amurka suka sha bamban a fannonin tsarin rayuwa da sauran fannoni da dama, irin wadannan bambance-bambance ba su shafi alaka da cudanya tsakanin kasashen biyu ba, don haka, bai kamata su shafi alakarsu a nan gaba ba.

Wang Yi, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da neman bunkasuwa da ci gaba don biyan bukatun al'ummominta tare da kara ba da sabbi da karin gudummawa ga rayuwar bil-Adama. Duk wani kokari na hana wannan mataki ba zai yi nasara ba. Ya bayyana cewa, a shirye bangaren kasar Sin ya ke ya shiga tattaunawa ta hakika da bangaren Amurka, tare da mayar da martanin da ya dace kan matakai marasa dacewa da damuwa na bangaren Amurka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China