Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD za ta taimakawa mutanen da aka yi fataucinsu a Najeriya
2020-08-06 11:29:02        cri
Hukumar kula da bakin haure ta MDD ta bude wata cibiya a jahar Edo dake kudancin Najeriya domin taimakawa harkokin shara'a ga mutanen da aka keta musu haddi ta hanyar fataucinsu a kasar ta yammaci Afrika.

A cikin wata sanarwar da hukumar ta IOM ta fitar, an ce, cibiyar shara'ar za ta samar da tallafi kyauta, da bada kulawa wajen gudanar da shara'ar ga mutanen da lamarin ya ritsa da su ba tare da la'akari da shekaru, ko jinsinsu ba.

IOM ta bayyana cewa, ta gudanar da shirin gangamin wayar da kan jama'a a jahohin Delta da Lagas dake Najeriyar.

Tony Ojukwu, babban sakataren hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya ya bayyanawa manema labarai a ranar 29 ga watan Yuli yayin bikin tunawa da ranar yaki da safarar bil Adama ta kasa da kasa cewa, Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da ake samun matsalar safarar bil adama. Don haka ya bukaci a gaggauta kammala shari'un dake da nasaba da batun fataucin bil Adama.

A bisa ga alkaluman binciken aikin bauta na duniya na shekarar 2018, Najeriya tana mataki na 32 cikin kasashen duniya 167 da suka fi yawan fataucin bil adama don aikin bauta inda ake samun mutane 7.7 cikin mutum 1,000 da matsalar ta ritsa da su. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China