![]() |
|
2020-08-04 21:00:35 cri |
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasarsa ta bukaci Amukra da ta gaggauta daina nuna wariya mai nasaba da siyasa ga kafofin watsa labarai da 'yan jaridun Sin dake kasar ta Amurka.
Kalaman Wang na zuwa ne, yayin da yake bayani kan yadda aka ki sabuntawa dukkan 'yan jaridun kasar Sin dake Amurka takardun neman viza da suka gabatar tun a watan Mayun da ya gabata.
A watan na Mayu ne dai, Amurka ta fitar da wasu sabbin ka'idoji, inda ta takaita ba da takardun iznin viza ga Sinawa 'yan jarida zuwa kwanaki 90 bisa yiwuwar kara musu wa'adi.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China