Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta sanar da cewa za ta dauki mataki kan wasu kamfanonin manhaja na Sin
2020-08-03 20:55:50        cri

A kwanakin baya ne kasar Amurka ta sanar da cewa, nan da kwanaki masu zuwa, za ta dauki mataki kan wasu kamfanonin manhaja na kasar Sin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana yau a gun taron manema labaran da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi kira ga wasu Amurkawa da su daina siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya, haka kuma su daina aiwatar da manufofin kyamar baki ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa.

Rahotanni sun nuna cewa, kwanan baya sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, gwamnatin Trump za ta dauki mataki kan wasu kamfanonin manhaja na kasar Sin wadanda ke kawo barazana ga tsaron kasar ta Amurka a cikin kwanaki masu zuwa, inda ya ambaci TikTok da WeChat.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China