Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta mayar da martani idan Amurka ta ci gaba da tsoma kan a harkokin cikin gidanta
2020-08-03 20:08:46        cri

Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka, da ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, idan kuma ta ci gaba da yin haka, hakika za ta mayar mata da martani.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, shi ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, a lokacin da yake mayar da martani kan takunkumin da Amurka ta sanyawa kayayyaki da masu aikin sa-kai na yankin Xinjiang(XPCC) da wasu jami'an kasar Sin guda biyu a yankin na Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin.

Wang ya ce, matakin na Amurka tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana ya saba muhimman ka'idojin alakar kasa da kasa, a don haka kasar Sin tana matukar adawa da ma Allah wadai da shi.

Jami'in na kasar Sin ya ce, batutuwan da suka shafi Xinjiang, ba su da alaka da hakkin bil-Adama, ko kabila ko addini, batu ne da ya shafi yaki da ta'addanci da 'yan aware. Haka kuma batutuwan yankin Xinjiang, batu ne na harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma Amurka ba ta da ikon tsoma baki a cikinsa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China