Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ayyana rufe ofishin jakadancin Amurka dake Chengdu
2020-07-24 13:29:22        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar da ofishin jakadancin Amurka dake nan Sin cewa, ta janye izinin da ya ba da damar gudanar da ayyuka a ofishin jakadancin Amurka dake birnin Chengdu na lardin Sichuan na kasar Sin. Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a Juma'ar nan, ta umarci da a dakatar da dukkanin wasu ayyuka a ofishin.

A ranar Talata 21 ga wata ne dai Amurka, ta ba da umarnin rufe ofishin jakadancin Sin dake birnin Houston, matakin da sanarwar ta bayyana a matsayin takala irin ta siyasa.

Kaza lika a cewar sanarwar, matakin na Amurka ya yi matukar keta dokokin kasa da kasa, da ka'idojin cudanyar kasashen duniya, da ma yaryeyeniyar da Sin da Amurka suka amincewa game da huldar jakadanci, baya ga lahanta kawancen kasashen biyu da matakin ya haifar.

A daya bangaren kuma, sanarwar ta ce martanin da Sin ta dauka halastacce ne, kuma yana bisa doka, ya kuma dace da ka'idojin kasa da kasa, da yanayin cudanyar kasashen duniya a diflomasiyyance. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China